Cikin yanayi na juyayi da ya kai ga zubar da hawaye daga mutane da dama, an gudanar da taron addu’o’in jana’izar mutanen da wasu ‘yan bindiga suka kashe a wata Coci da ke garin Owo a jihar Ondo.
A ranar 5 ga watan Yuni, ‘yan bindigar suka kai hari Cocin Saint Francis Catholic Church da ke garin na Owo a kudu maso yammacin Najeriya inda suka datse kofar Mujami’ar suka bude wuta.
Akalla mutum kusan 40 suka mutu.
Jana’izar ta samu halartar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu da mai dakinsa Chief Betty Anyanwu wacce aka yi a Mydas Resort Hotel da ke garin na Owo kamar yadda wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar dauke da sa hannun Sakataren yada labarai Richard Olatunde ta fada.
Gwamna Akeredolu, wanda ya zubar da hawaye yayin taron addu’o’in ya nuna gazawar gwammati wajen kare jama’a daga wannan aika-aika.
“Mun gaza kare wadannan mutane, ba wai don ba mu gwada yin hakan ba, sai dai don wadanda suka aikata wannan danyen aiki suna da goyon baya, ba za su taba yin nasara akanmu ba.” Akeredolu ya ce.
Akeredolu ya kara da cewa, akwai bukatar mahukunta su yi wani, yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi garambawul ga fannin tsaron Najeriya.
Yayin nasa jawabin, Limamin Mabiya darikar Katolika a jihar Ondo, Dr. Jude Arogundade, ya bayyana cewa Gwamna Akeredolu bai gaza wajen kare al’umar jihar ba.
Akalla mutum 22 aka yi wa jana’iza a ranar ta Juma’a duk da cewa mutum 41 aka tabbatar da sun mutu a harin.
“Mamata 22 ne a wannan dakin taron. An riga an binne wasu kalilan, saboda ‘yan uwansu sun ce ba za su iya jira har zuwa yau ba, amma a kididdiga ta karshe da muka yi, mutum 40 aka kashe.” In ji Akeredolu.