An Yi Hadarin Jirgin Ruwa a Chana

Jami'ai a Hong Kong sun fara neman wadanda hadarin jirgin ruwa ya shafa.
Jami’an ayyukan ceto sun sami sukunin isa tsallaken gabar ruwan teku a Hong Kong, sun kuma fara neman ma’aikatan jirgin ruwan nan su goma sha daya da suka bace a jirgin ruwan daukan kayan China wanda yayi hatsari har ya kai ga nutsewa a teku bayan cin karon da yayi da wani makeken jirgin ruwan daukan kaya.

Anji jami’an ayyukan jiragen ruwan Hong Kong na cewa karamin jirgin ruwan kamun kifi yaci sa’ar ceton mutum guda bayan cin karon da yayi da makeken jirgin ruwan yana dab da nutsewa. Jami’an ayyukan kula da jigilar jiragen ruwan naci gaba da gudanar da ayyukan ceto yau litinin daga sassa dabam-dabam a kudancin ruwan tekun China. Jami’an suka ce jirgin ruwan daukan kayan da ya nutse mai tsahon mita 97 anyi rajistarsa ne a China.