Hukumar kula da harkokin ruwa da yanayi ta Najeriya ta gudanar da taron yawar da kawunan jama'a akan illar ambaliyan ruwa
Taron ya kunshi masu ruwa da tsaki da suka hada da masana kan lamuran albarkatun ruwa da raya gandun daji, da kwararraru kan harkokin muhalli da sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati kan sha’anin tsara birane kana da kungiyoyin kare muhalli da dakile afkuwar annoba.
Injiniya Yunusa Yahaya Ashiru shine daraktan shiyyar Kaduna na hukumar kula da harkokin ruwa ta najeriya ya fayyace abubuwan da taron ke muradin cimmawa.
Dr Ibrahim Yakubu Tudunwada na hukumar bincike kan harkokin kasa da sararin samaniya ta hanyar tauraron dan adam na cikin wadanda suka gabatar da makala.
Alhaji Ahmed Garba, Sarkin Bichi a jihar Kano yace sarakunan gargajiya na taka rawa wajen fadakar da al’umma kan raya bishiyoyi a matsayin matakin kare hamada, zezayar kasa da ambaliyan ruwa.
Taron dai na zuwa ne mako guda bayan da hukumar NEMA mai bada agagjin gaggawa a Najeriya tayi gargadin cewa, akwai yuwuwar ambaliyan ruwa a wasu jihohi 8 na kasar, kuma galibinsu na daga yankin arewa.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5