Wata kungiya mai fafautikar kare hakkin bil Adama musamman mata da yara ita ce ta shirya gangamin fadakar da al'umma akan illar cin zarafin mata da yanzu yake son ya zama tamkar ruwan dare gama gari.
Shugaban kungiyar Dr Joe Odumakin ya yi karin bayani game da gangamin. Yace muzgunawa mata na karuwa a kasar. Kawo yanzu mata ukku sun rasa rayukansu saboda ukubar da suka sha walau daga mazajensu ko wasu daban. Saboda haka akwai bukatar wayar da kawunan al'umma tare da bukatan gwamnati ta dauki matakai domin kare mata da yara.
Alkalumma sun nuna cewa kashi biyu cikin ukku na mutanen da ake muzgunawa mata ne. Dalili ke nan da wani namiji yace akwai bukatar wayar da mutane, musamman maza, akan illar muzgunawa mata da yara.
Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5