An Yi Bukukuwan Tunawa Da Gudunmowar Matan Karkara a Duniya

Matan karkara na taka rawa a harkokin tattalin arziki sosai

Hankali ya sake komawa kan irin namijin kokarin da matan karkara ke bayarwa musamman ma a fannin noma da tattalin arziki da zamantakewa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonia Gutarres ya yi kira ga gwamnatocin duniya da su bayar ba batun kare hakkokin mata muhimmnacin. Gutarres ya yi wannan kiran ne albarkacin ranar mata ta duniya ta shekara-shekara.

Taken ranar ta wannan shekarar shi ne: Samar da Tabbataccen Tsari na Kawar da Wariyar Jinsi Domin Cigaban Mata da 'Yan Mata a Karkara Domin Cigaban
Karni.

Gutaress ya ce mata, a ko ina suke, a samar masu da filayen noma da kuma tsare su daga daga ukuba irin su fyade da musgunawa da kuma basu ilimi da domin samun nasarar cimma sabon shirin muradun karni na mdd, domin kawar da talauci a tsakanin al’umma.

Wannan kuwa, inji babban sakataren, zai samu ne idan aka saka mata cikin
sauran al’amuran daya shafe su, bawai su zama yan kallo ba a harkokin
mulki da siyasa.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen duniya da hatta matan birni
ke neman samun yanci ballantana na karkara, To sai dai game da zargin ba’a baiwa mata dama a harkokin mulki, wani dan siyasa mai Usman Musa Garba yace laifinsune domin mata ma basa zaben mata yan uwansu balle maza su zabe su.
Yanzu dai a yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana domin
gudunmowar matan karkara, abin jira a gani shine rawar da hukumomi da
sauran jama’a zasu taka wajen habakan rayuwar mata da 'yan matan
karkara.

Ga dai wakilinmu a Lagos, Babangida Jibrin, da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Matan Karkara Ta Duniya