Kiyasin hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya dai ya nuna cewar kimanin mutane dubu dari hudu ke mutuwa a duk rana, a sakamakon kamuwa da cutuka dake da nasaba da rashin guraren ba haya mai tsafta.
Asusun tallafawa kanan yara ya UNICEF shinma ya ce miliyoyin yara na mutuwa sakamkon kamuwa da cutuka daban daban saboda rashin tsaftace bahaya. Har ila yau hukumar ta lafiya tace mutane biliya hudu da rabi ke zaune a gidajen dabasu daguraren bahaya mai tsafta a gidajensu.
A Najeriya kuma bincike ya nuna cewar mutane kusan miliyan bakwai ne ke ba haya a filayen Allah abinda kuma ke taimakawa wajen yada cutuka musanman ga yara kananan da mata masu juna biyu.
Wani dan najeriya mai suna Danladi Aboki yayi tsokaci game da wannan ranar yace maganar guraren ba haya ko magunan ruwa a Najeriya an bada talakawa, domin idan aka duba inda talakawa ke zaune a gidajen haya akwai karancin guraren ba haya.
Your browser doesn’t support HTML5