An Yi Bukin Baje-Kolin Takalmi Da Rigar Da Pgba Yasa

Dan wasa Paul Pgba

Wasu rahotanni sun bayyana cewar a wani bikin baje koli kayayyaki da akayi a birnin Faris ranar Litinin 29 ga watan Afirilu 2019, an sayar da Takalmin kwallon da dan wasan Faransa, Paul Pogba yasa ya buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya da shi a Rasha bara, akan farashin Euro dubu €30, dalar Amurka dubu ($33,470) kimanin Naira miliyan 12 da dubu 60.

Dan wasan Pogba, wanda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, shi ya jefa kwallo ta uku a wasan da Faransa ta doke
Croatia daci 4-3, a gasar ta cin kofin duniya, wace kasar ta Faransa ta lashe a bara.

Daga farko dai an kiyasta darajar Takalmin a kan kudi Euro dubu €35 zuwa dubu 50.

Bayan haka kuma an sayar da wata rigar kwallon da Pogbaya sanya ta a fafatawar da Faransa ta lallasa kasar Iceland a matakin wasan daf da na kusan karshe, Quarter final a gasar cin kofin kasashen Turai na shekarar 2016 akan farashin Euro dubu €4.

Bayan kammala bukin na baje kolin, dan wasan Pgoba yace ya sadaukar da kudin da aka saye takalmin zuwa ga gidauniyar agaji don tallafawa daliban makarantun boko dabasa da hali.

Har ila yau akwai wata rigar da aka mata darajar kudi euro dubu €3, wadda ya sanya a yayin wasansu da kasar Holland, na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata.