Zaman tattaunawa da rungumar juna ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, na daga ginshikin zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al’umma.
A bikin ranar zaman lafiya ta duniya da aka gudanar a garin Jos, al’umma da dama sun bayyana cewa akidar yafiya tsakanin wadanda suka sami sabani a baya, zai taimaka wajen samun dawwamammen zaman lafiya da ci gaban kasa baki daya.
Basarake a yankin Rantya-gyel da ke Karamar Hukumar Jos Ta Kudu, Da Dalyop Pam, ya ce, duk da rikcin da aka samu a unguwannin makwabtansu, sun dauki matakan tattaunawa tsakanin Kirista da Musulmi don haka su ke zaune lafiya da juna.
Abdullahi Rocky Boy, da ke fafutukar wanzar da zaman lafiya a garin Jos, ya ce, dole iyaye su dukufa wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu.
Shugaban kungiyar matasan Fulani ta Jonde Jam, Alhaji Saidu Maikano, ya ce, ci gaba na samuwa ne idan al’umma sun zauna lafiya.
Sakataren gwamnatin jahar Filato, Farfesa Danladi Atu, ya ce, gwamnati na kokarin hada kan jama’a.
Ga cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, daga Jos.
Your browser doesn’t support HTML5