Wani dan Majalisar Dattawan Najeriya ya yi bayanin dalilin da ya sa aka canja tsarin tantance Ministoci a Majalisar Dattawan Najeriya ta yadda a maimakon goma a yanzu ake tantance uku kawai a rana. Da ya ke bayani ma wakiliyar Sashin Hausa Madina Dauda, Sanata Ali Ndume ya ce abin da ya sa aka canja tsarin shi ne mutane sun yi korafin cewa tantance Ministoci goma a rana ya yi yawa. Y ace su kansu ‘yan Majalisar wasunsu na korafin cewa bas u samun damar yin tambayoyi ga wadanda ake tantancewar saboda sun yi yawa.
Sanata Ndume y ace saboda korafin na jama’a da ‘yan Majalisar Dattawan sai aka yanke shawarar cewa dayake saura mutane goma sha takwas a tantance, za su dau mutane uku-uku cikin gwanaki shida da ake zama za a dau sati biyu a kammala tantancewar. Ya ce wannan zai ba su damar duban sauran ayyukan Majalisar tunda ba aikinsu shi ne tantance Ministoci kawai ba. Ya ce akwai wasu kudurorin da aka gabatar da ke bukatar dubawa baya ga batun tantance Ministocin.
Game da batun kurar da ta taso game da batun tantance tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi, Santa Ndume y ace sun a kan ba da hakuri shi ma ya na tattaunawa da su dayake batu ne na siyasa. Ya ce za su gabatar da shi koma kuma da yaddar Allah ba za su sami wata matsalaba. Ya ce sabanin kama karyar da y ace an yi a gwamnatin PDP a yanzu so su ke su bi tsarin da ya dace da doka. Amma ya ce idan kura ta kai bango, to za su nuna ma ‘yan adawa cewa su ke da rinjaye.
Ga Madina Dauda da cikakken labarin:
Your browser doesn’t support HTML5