Daidaikun ‘yan Najeriya da kungiyoyi na bayyana takaicinsu da yadda ‘yan Majalisar Tarayyar Najeriya ke nuna son zuciya gaba da komai musamman yadda su ke ribibin zama mambobin kwamitocin da aka fi samun abin duniya a maimakon kare muradun ‘yan Najeriya ko kuma wadanda su ka zabi wakilan. Hasali ma, masu lura da al’amuran yau da kullum na bayyana takaicinsu kan yadda ‘yan majalisar tarayya kan kwashe lokaci mai tsawo ba tare da yin wani abin kirki da ya shafi jama’a ba.
A hirarsu da wakiliyarmu a Abuja, Madina Dauda, masani a fannin diflomasiyya tattalin arziki da zamantakewa, Mainasara Ibrahim Faskari ya ce abin takaici ne ace wai ma har wasu ‘yan majalisa na kin aiki a wasu kwamitocin majalisar wadanda ake ganin bas u da romo. Don haka a cewar Madina “Matakin da wadansu yan Majalisa suka dauka na kin karbar mukaman komitoci ya bude sabon babi ne a harkar gudanar da ayyukan sa ido da akan sa yan Majalisar yi wanda kuma shi ne muhimmi a ayyukan da za su taimaka wa al'ummar kasa.”
Shi ma Shugaban kungiyar “Progressive Mind for Development Initiative” Kwamrad Abubakar Abdulsalam, y ace wannan al’amari na kin karbar aikin kwamitin da ake masa ganin mara romo, ya tabbatar da wani abu ne da tun da ma ake da masaniya game da shi na zalama tsakaninwasu ‘yan Majalisar Tarayyar Najeriya. Don haka ya na mai kira ga masu kada kuri’a su rinka zaban mutane masu kishin kasa a maimakon mahandama.
Ga Madina Dauda da cikakken labarin:
Your browser doesn’t support HTML5