An Yanke Ma Barawon Kaji Hukuncin Aikin Kwadago A Lagos

A yau Jumma'a ne wata kotu a jihar Lagos ta yanke ma mani matashi dan shekaru 25 da haihuwa mai suna Omotayo Lawal, hukuncin yin aikin awoyi goma goma saboda satar kaji 14 daga wasu gidajen kaji biyu da ya yi.

Alkalin Kotun, Mr O. O. Olatunji, ya yanke wa Mr. Omotayo hukuncin ne bayan da shi Omotayo ya amsa cewa lallai ya aikata laifukan biyu. Mr Olatunji ya ce, mai laifin zai gudanr da ayyukan da suka hada share-share, da sauransu na awoyi goma - goma akan laifukan biyu.

Alkalin ya kuma yi wa Omotayo kashedin kada ya sake aikata wani abu mai kama da haka nan gaba, don ba za a yi masa afuwa ba.

Omotayo Lawal dai ya nemi a yi mashi afuwa, tare da yin alkawarin ba zai kara yin sata ba.

An fadawa wannan kotun cewa Omotayo, mazaunin unguwar Erikoko ne a karamar hukumar Ikorodu, ta jihar Lagos, kuma a nan uguwar gidajen kajin suke.

Omotayo Lawal dai ya saci kaji 6 daga gidan kajin Mr. Olayinka Adeyemi, bayan haka ya saci wasu guda 8 daga gidan kajin Bisi Ashima ranar 19 ga watan nan na Oktoba.

Nan take dai aka mika wa Omotayo tsintsiya ya fara share harabar kotun.