An samu yankewa babban madugun kwayar nan na kasar Mexico, Joaquin Guzman wanda aka fi sani da “El Chapo’ hukunci, akan laifin safarar kwaya da sauran wasu laifuka a birnin New York.
A ranar Talatar da ta gabata Masu shari'ar sun yanke hukunci, bayan kwanaki shida suna tattaunawa a kan dukkanin laifuffuka goma da ake zargin sa dasu. kuma yanzu akwai yiyuwar zai zauna a jidan yari har karshen rayuwar sa.
Watanni uku da kawo ƙarshen shugabancin Guzman na kungiyar masu sai da miyagun kwayoyi wato Sinaloa Cartel, wanda masu gabatar da kara sukace itace "mafi girma a duniya."
Masu gabatar da kara na tarayya sun ce, nasarar da Guzman ya samu ya fara ne a shekarun 1980, lokacin da kwarewar da yayi a cinikayar hodar ibilis wato "cocaine" zuwa cikin Amurka, ya samar da kudaden ga jami'an kwastan na Colombia.