Zai Kwashe Shekaru Biyu Da Rabi A Gidan Yari Akan Satar Takalma

Wata kotu da take zama a Rijiyar Zaki, a birnin Kano ta yankewa wani matashi Rabiu Sani, mai shekaru ashirin da biyu hukuncin shekaru biyu da rabi a gidan yari a bisa satar takalmi.

Mai shara’a, Aminu Fagge, ya yanke hukuncin ne baya da Rabiu Sani, mazaunin unguwar Aisami, ya amsa laifin sata, ya kuma yanke hukuncin ne ba tare da bashi zabin tara ba.

Mai gabatar da kara Yusuf Sale, ya ce takaman da ya sata an bada jimillar su akan Naira dubu shida.

Mai gabatar da karar ya ce a can baya ranar 5, ga watan Fabarairu, na wannan shekarar an yankewa Rabiu Sani, hukuncin watani ukku ko kuma tarar Naira dubu goma, a bisa samun sa dalaifin sata, aka kuma sake yanke mashi hukuncin watani shida ko tarar Naira dubu ashiri, a watan Afirilu duk a wannan shekarar shima akan sata.

Mai gabatar da karar yace wannan shine karo na hudu da ake gurfanar da Rabiu Sani, a gaban shara’a, akan sata a wannan shekarar kawai.