Wata kotun yaki da almundahana da ke kasar Pakistan ta zartas da hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ma tsohon Firaminista Nawaz Sharif, tare kuma da cinsa tarar dala miliyan 10.5 saboda kasa bayyana yadda ya mallaki dinbin dukiya a kasashen waje.
Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 7 ma diyarsa, wacce kuma ta gaje shi a siyasance wato Maryam Nawaz, baya ga tarar da aka ma ta sama da dala miliyan 2.5, saboda laifin hadin baki mai nasaba da boye dukiyar da uban ya mallaka a kasashen waje. Shi kuma mijinta an yanke masa hukuncin daurin shekara guda.
Su ma 'ya'yan Sharif biyu, wato da Hassan Nawaz da Hussain Nawaz, na cikin wadanda aka kai kara. Masu gabatar da kara sun ce tun daga farko yaran su ka ki gabatar da kansu ga kotun, saboda haka za a yanke masu hukunci duk kuwa da ba su nan.