Rundunar sojojin Najeriya ta ce an kashe wasu ma’aikata dake aikin gini a yankin arewa maso gabashin kasar, a inda ‘ya’yan kungiyar nan ta Boko Haram suka fi karfi.
Jami’an soja suka ce wadannan mutane da aka kashe su na daga cikin masu aikin gina babban masallacin Jumma'a na garin Maisduguri.
Wani kakakin soja ya fadawa kamfanin dillancin labaran Asasociated Press cewa an yanka wadannan mutane guda tara ne cikin dare a gidan da suke kwana a wata unguwa mai suna Bolori a garin na Maiduguri.
Jami’ai ba su fadi wanda ya kashe wadannan mutane ba. Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ya sha fuskantar hare-hare daga ‘yan kungiyar Boko Haram.
Kungiyar ta dauki alhakin kai hare-hare da dama a Najeriya, ciki har da hare-hare kan majami’u da wani gini na Majalisar Dinkin Duniya.