An Yabawa NFF Kan Nada Sunday Oliseh A Matsayin Koch Din Super Eagles

File: In this Monday, June 30, 2014 file photo, Nigeria's Emmanuel Emenike, center, looks up as his team form a huddle before the start of the second half during the World Cup round of 16 soccer match between France and Nigeria at the Estadio Nacional in

Masu ruwa da tsaki kan harkar kwallon kafa a jihar Enugu, sun yabawa hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF a takaice, kan nada Sunday Oliseh a matsayin sabon koch na kungiyar Super Eagles.

A lokacin da suke magana da kamfanin dillancin labarun Najeriya, sunce mika wannan mukami ga Oliseh shine zai kawo karshen matsalar koch da ake fuskanta a kungiyar Super Eagles.

Daraktan wasanni na jihar Enugu, John Eli, yace wannan mukami ya dace da Oliseh idan aka duba irin sanin sa da horon sa a kwallon kafa. Ya ci gaba da cewa, “kamar yadda a baya yeka matsayin kaftin na Super Eagles, ya kuma je neman ilimi irin na koch, yana da ginshiki mai kyau, bashi wannan mukami NFF tayi abin azo a gani.”

Ya kara da cewa irin wannan zabi shine zai karawa matasa kwarin gwiwar yin aiki tukuru don ganin zasu iya cimma bukatun su nan gaba.

Dayawa daga cikin masu ruwa da tsakin sun fadi albarkacin bakin su kan nada Sunday Oliseh matsayin koch din Najeriya, sun kuma yi masa murna da fatan Allah ya bashi damar yin aikin da ya kamata, wanda zai taimakawa ‘yan wasan Najeriya ga cimma burunsu a wasanni masu zuwa.