An Yaba Da Yadda Mai Tsaron Raga David de Gea Ke Tsaron Gida

Kocin rikon kwarya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Sloskjaer, yace tabbas mai tsaron raga na kulob din David de Gea zai iya kafa kansa a matsayin mai tsaron raga mafi girma a kungiyar.

Sloskjaer ya fadi hakane bayan da aka tashi a wasan da Manchester United ta doke takwararta Tottenham daci daya mai haushi ranar Lahadi, cikin wasan mako na 22 a bangaren firimiya lig na bana a Wembley.

Inda David De Gea ya tsare kwallaye 11 wanda ya kamata su fada ragar Manchester, a yayin wasan inda ya tsare kwallaye mafi yawa a wasan firimiya har guda 11 a wasa daya.

Sloskjaer yace a yayin da yake matsayin dan wasa wanda ya shafe shekaru 11 tare da manyan masu tsaron raga irin sau Edwin Van der Sar da kuma
Peter Schmeichel, a Manchester United, David De Gea zai iya kalu balantarsu nan gaba kadan.

David De Gea mai shekaru 28, da haihuwa dan kasar Spain ya taho Manchester United ne daga Atletico Madrid, a shekarar 2011, ya kuma lashe kyautar dan wasa mafi kwazo na shekarar da kungiyar take bayarwa cikin shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata.

Bayan haka a wasan da aka buga da Tottenham ranar Lahadi ya kasance dan wasan da aka zabe shi mafi kokari, inda kocin na Manchester yace dan wasan ya cancanta da kyautar.

David De Gea ya tai maka wa kungiyar wajan samun nasa a wasanni shida a jere kar kashin kocin Ole Gunnar Sloskjaer.