A taron manema labarai babban magatakardan hukumar a Najeriya Farfesa Abdulrasheed Garba yace sakamakon ya nuna sama da kashi 68 na wadanda suka rubuta jarabawan sun samu nasarar da ake bukata a darasin turanci da lissafi. Wanda wannan ya nuna cewa jarabawar ta bana an samu ci gaba.
Farfesa Abdulraseed Garba yace akwai dabarun da hukumar
tayi a lokacin jarabawar.
‘’Abinda muka yi shine muka tabbatar cewa duk tambayar da za ayi to ta fito daga cikin abubuwan da aka amince a koyar a makarantun sakandare, wannan yasa muka samar da dangantaka tsakanin hukumar ta NECO da hukumar NRDC, Wannan hukumar ta NDRC ita ce keda allhakin fitar da jadawalin koyarwa’’
A wannan shekarar kuma satar jarabawar bai kai na shekar bara ba.
‘’Labari mai dadi shine magudin da aka samu a wannan shekar bai kai na bara ba domin duk dabarar da kayi sai ka samu magudi amma wanna shekarar bai kai na bara ba, duk da haka mun kakkama an tantance kuma an zakulo wadanda suke da laifi da yawa an soke sakamakon su.’’
Sai dai ya zuwa wannan lokaci hukumar ta NECO tace tana bin wasu jihohi bashin kudin jarabawan su da basu biya ba, kamar yadda Farfesa Abdulrasheed yayi Karin bayani.
Ga Mustafa NasirBatsari da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5