A Najeriya Sashen Hausa na Muryar Amurka ne ya samu lambar yabo, daga wata Kungiya mai zaman kanta mai suna NULGE wace ta bayyana gamsuwa da yadda VOA ke tsage gaskiya komin dachinta, waye lamarin ya shafa.
Kungiyar NULGE, kungiya ce ta Ma'aikatan Kananan Hukumomi a Najeriya, wacce ta ke bukin cika shekaru 40 da kafuwa.
A yayin da Kungiyar ta shirya wannan buki na mika lambar yabon, an yi katarin ziyarar aiki da babban Editan Sashin Hausa Aliyu Mustapha Sokoto ya kawo a Abuja Birnin Taraiyyar Najeriya, a saboda haka shi ne ya amshi takardar shedar yabon.
Aliyu ya bayyana rabon da abin alfahari ga Sashin Hausa na Muryar Amurka irin wannan ya faru an dade, inda ya ce yana nuni da cewa Sashin Hausa na yin abinda ya kamata, wajen ilmantar da mutane musamman ma wadanda ke zaune a Karkara da birane da ma duniya baki daya.
Aliyu Mustapha ya yi godiya ga Shugaban Kunyar ta Kasa Komred Ibrahim Kaleel da Babban Bako Mai Martaba Shehun Borno Abubakar Umar Garbai Elkanemi, da Shugabanin Majalisun jihohin Bauchi, Kwara, Bayelsa da suka halarci taron.
Su ma Ma'aikatan Sashin Hausa da aka yi taron a idanun su wanda suka hada Auwal Salihu, Hauwa Umar, da Hassan Maina Kaina, sun yaba da samun lambar yabon inda suke ce zai kara masu karfin gwiwa wajen yin aiki tukuru domin ilmantarwa da kuma wayar da kawunan al'umma.
Your browser doesn’t support HTML5