Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tura dan fafutuka kuma dan jarida Moussa Tchangari Gidan yarin Flingue da ke a tazarar km 180 a arewa maso gabascin Birnin Yamai.
Moussa Tchangari wanda ya shafe kusan wata 1 a hannun ‘yan sandan yaki da ta’addanci ya yi fice wajen sukar lamirin gwamnatin mulkin sojan Nijer.
Ya gurfana a wata kotun birnin Yamai a yammacin Juma’a 3 ga watan Janairu 2025 inda alkali ya saurare shi.
A farkon watan Disamban 2024 ne wasu mutane dauke da bindigogi suka kutsa gidan sakataren kungiyar Alternative Espace citoyen, Moussa Tchmgari, suka kuma yi awon gaba da shi jim kadan bayan dawowarsa daga wata tafiyar da ta kai shi biranen Abidjan babban birnin Cote d’ivoire da Abuja Najeriya kafin daga bisani a ji duriyarsa a cibiyar 'yan sanda yaki da ta'addanci.
Karon farko an gabatar da shi a kotun Tribunal a yammacin Juma’a 3 ga watan Janairu inda alkali ya saurare shi kafin a yi gaba da shi.
Ainahi ana zargin Tchangari da kafa kungiyar ta'addanci da tallata ayyukan 'yan ta'adda kafin a bullo da wasu karin zarge-zargen na daban da ke da nasaba da sha’anin tsaron kasa lamarin da ke daure kan lauyoyinsa da na hannun damansa.
Moussa Tchangari wanda a fili yake nuna goyon baya ga hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yi fice wajen caccakar gwamnatin Janar Abdourahamane Tiani saboda yadda ya yi imani kan mulkin dimokradiya.
Kulle shi a kurkuku abu ne da wasu ke dauka a matsayin bita da kulli a yunkurin rufe masa baki.
Ba a dai yanke masa hukunci ba saboda haka ana sa ran sake gabatar da shi a gaban alkali a nan gaba.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5