Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar tsaro ta farin kaya, wacce aka fi sani da Civil Defence a turance, ta tura jami’anta 1,200 zuwa sassan jihar Borno da aka kubutar daga hannun mayakan Boko Haram.
Daukan wannan matakin a cewar babban kwamandan rundunar tsaron ta farin kaya, Muhammadu Gana, shiri ne na karawa fararen hula kwarin gwiwar sakewa su gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
“Mutane sun yi murna, inda suka ce lallai yanzu suka san cewa gwamnati ta damu da zaman lafiya, tun da har na ziyarci mutane na da ke wurin.” Inji Gana yayin da yake ganawa da Muryar Amurka a lokacin ziyarar da ya kai a jihar ta Borno.
Jihar Borno ta kasance tungar Boko Haram inda dubban mutane suka rasa rayukansu kana aka rasa dumbin dukiyoyi.
Rikicin na Boko Haram ya kai ga wasu yankunan jihar sun fada karkashin ikon ‘yan ta’adda a shekarun baya, amma dakarun Najeriya sun karbo wadannan yankunan kamar yadda rahotanni ke nunawa.
Lamarin da ya bai wa mazauna yankunan kwarin gwiwar komawa gidajensu.
Baya ga rikicin Boko Haram, ana sa ran jami'an tsaron za su mayar da hankali wajen yakar matsalar rikicin makiyaya da manoma a jihar ta Borno.
Saurari cikakkiyar hirar wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu da kwamandan rundunar tsaron ta farin kaya, Muhammadu Gana:
Your browser doesn’t support HTML5