An tuna da mutuwar Micheal Brown a Ferguson

Mahaifin Micheal Brown (Tsakiya) a Wajen Zanga-Zangar Tunawa Da Marigayin Dansa

Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zanga a jiya Asabar a garin Ferguson dake Jihar Missouri anan Amurka don yin tunawa da kisan da farar fatar Dan Sanda ya yiwa wani yaro marar makami.

Masu rajin kare ‘yancin bil’adama da malaman addini ne suka yi cincirundo mafi yawancin su bakaken fatar Amurka a birnin da ya fi yake dauke da mafi yawancin bakaken fata. Macin da aka yi shi karkashin jagorancin mahaifi da sauran iyalan mamacin Micheal Brown dan shekaru 18 a duniya.

Mutuwarsa a ranar 9 ga watan Agustar bara ya tada bore na tsawon kwanaki a birnin. Daga baya kuma aka ci gaba da zanga-zangar watannin bayan masu yanke hukunci sun ki bawa farar fatar dan sanda laifin kisan kan.

Ana zaton yau Lahadi, yawan jama’ar zai karu, a inda za su taka salin-alin har zuwa Coci don yin bauta tare da addu’oi. Mahaifin Micheal Brown ya fadawa manema labarai a jiya Asabar cewa, zai yi iyakar kokarinsa don raya mutuwar dansa saboda ceton ‘yan baya.

Sannan wasu zasu yi tsit na tsawon minti 4 da rabi, a matsayin girmamawa ga sa’o’I 4 da rabi da shi Micheal Brown yayi a mace bayan an harbeshi akan titi kafin a dauke gawarsa.