Wannan ne karon farko da dokar za ta fara aiki, tun bayan da aka samar da ita a shekarar 2002, wato bayan harin da kungiyar Al Qaeda ta kai a New York da Washington a shekarar 2001.
WASHINGTON D.C. —
Hukumomi a kasar New Zealand, sun tuhumi mutumin nan mai fafutukar ganin an fifita farar fata, wanda ya kashe mutum 51 a wasu masallatai da ke garin Christchurch a watan Maris din da ya gabata.
A yau Talata aka tuhumi Brenton Tarrant dan asalin kasar Australia da laifin ta’addanci.
Wannan ne karon farko da dokar za ta fara aiki, tun bayan da aka samar da ita a shekarar 2002, wato bayan harin da kungiyar Al Qaeda ta kai a New York da Washington a shekarar 2001.
Hukumomi har ila yau, sun caji Tarrant da laifin mutuwar wani da harin ya rutsa da shi, wanda ya cika a asibiti a wannan watan, hade da tuhumar shi kan yunkurin kashe mutum biyu, wanda ya sa adadin ya kai 40.