An Tsige Shugaban Majalisar Dokoki A Jihar Adamawa

An Tsige Shugaban Majalisar Dokoki A Jihar Adamawa

‘Yan Majlaisar dokokin jihar Adamwa, sun kada kuri’ar amincewa tsige shugaban majalisa Ho. Ibrahim Sadiq da mataimakiyarsa Hon. Wale Fwa litinin da ta gabata. ‘Yan Majalisar sun bada hujjar cewa shugaba da mataimakiyarsa sun gaza aiwatar da ayukan mulkin majalaisar yadda ya kamata.

Saurari:

Makonni shida kafin zaben Gwamna a jihar Adamwa, Nigeria ‘yan majalaisar dokokin jihar suka kori shugaban majalisar shi da mataimakiyarsa. Rahoton da wakilin sashen hausa na Muryar Amurka a Yola, babban birnin jihar Adamwa Ibrahim Abdulaziz ya aiko na cewa, shugaban da mataimakiyarsa sun kasa hada kan ‘yan majalisaar wajen tinkarar matsalolin da ake fuskanta game da tsara kuduri ko matsalar samar da kayan aiki a majalisar yadda ya kamata. Haka na farauwa ne kafin zaben Gwamnan jihar da ake shirin. Amma masu sukan lamirin tsige shugabannin majalisar dokokmin na jihar Adamwa sun koka da acewar an tsige shugabannin ne saboda an fahimc I basa goyon bayan sake maida Gwamnan jihar a zaben da ake shirin yi.

Aika Sharhinka