An Tsige Gwamna Murtala Nyako

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa

Kakakin majalisar ahmad ahmadu pintrir shine ya maye kujerar mukaddashin jihar adamawar.

Cikin tsauraran matakan tsaro yan majalisar dokokin jihar Adamawa suka yi zama na musamman. Kakakin majalisar dokokin jihar Ahmad Ummaru Pintiri, na daya daga cikin yan majalisa goma shatakwas da suka yi zaman. Inda suka amince da binciken kwamitin da aka kafa wanda hakan ya kawo batun tsige gwamann jihar adamawar Murtala Nyako.

Zaman yan majalisar ke da wuya, sai kakakin majalisar Ahmed Ummaru Pintiri ya karanto wasikar murabus daga mataimakin gwamnan jihar John Bala Gilari. Wanda hakan ya sa ba a ma tabo batun mataimakin gwamnan ba a rahoton binciken.

An tsaige gwamna Murtala Nyako kamar yadda doka ta tanadar, kakakin majalisar Ahmad Ummaru Pintrir shine ya maye kujerar gwamnan jihar ta Adamawa. Kuma nan ba da jimawa ba ake sa ran zai yi wa al’ummar jihar jawabi. To ko yaya yan bangaren Nnyako suka dauki wannan al’amari?

Darektan yada labaran bangaren Nyako, Alhaji Ahmad Sajoh ya yi bayani akan al’amarin inda yace, “abu na farko shine Allah Ya sani ba a bi doka da ka’idodin tsarin mulki ba, ko umurnin kotu a wannan matakin da aka dauka”. Kamar yadda zaku ji bayani a cikin rahoton da wakilin sashen hausa na muryar Amurka a Adamawa Ibrahim Abdu'aziz ya aiko.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tsige Gwmana Murtala Nyako - 0'57"


`