An Tsaurara Matakan Kariya a Filin Jiragen Saman Kano

Lokacin da ake duba yanayin jikin wasu matafiya a filin jiragen saman kasar Haiti.

Kwana guda bayan da hukumomin lafiya a jihar Kano suka yi alkawarin daukar matakan kariya daga cutar Coronavirus, Jami'an kiwon lafiya da na tsaro sun kara tsaurara matakan bincike a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Da marecan jiya ne Jami'an lafiya suka kwashe sa'o'i da dama suna aikin gwajin cutar akan fasinjojin wani jirgin sama, mallakar kamfanin Ethiopia wanda ya yada zango a birnin Adis Ababa bayan tasowar shi daga birnin Jeddah kafin ya sauka a Kano.

A wurin binciken Fasinjojin su kimanin 500 wakinlinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya tattauna da wasu daga cikinsu.

Sun sheda masa cewa yadda aka dinga gudanar da bincike a kansu, ko a filin jiragen saman Addis Ababa ba a gudanar da bincike kansu haka ba.

Wannan matakin na zuwa ne kwannaki kadan bayan da aka samu bullar cutar Coronavirus ta farko a Najeriya.

Lamarin ya saka tsoro a zukatan mutane da dama a kasar, duk da dai shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira gare su, da su kwantar da hankulansu.

Latsa kasa domin sauraran muryoyin wadanda wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya yi hira da a filin jiragen saman.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tsaurara Matakan Kariya a Filin Jiragen Saman Kano 4'52"