Jami’an kasar Belarus sun ce, a yau Talata an tsare Maria Kolesnikova, wata jagora a bangaren adawar kasar a lokacin da ta yi kokarin shiga kasar Ukraine.
Jami’an sun ce Kolesnikova na tafiya ne tare da wasu mambobin bangaren ‘yan adawa su biyu a lokacin da lamarin ya faru, Anton Rodnenkov da Ivan Kravtsov, wadanda dukansu biyu suka yi nasarar shiga Ukraine.
Ba a bayyana yadda tawagar ta su ta kai iyakar kasar ba.
Mataimakin Ministan harkokin cikin gida na Ukraine, Anton Gerashchenko ya bayyana a shafinsa na facebook cewa abinda ya faru a yau ba da son rai ba ne, illa kawai abin da ya kira kora ta karfi da yaji.
Wannan lamarin dai ya janyo kiraye kiraye daga kasar Jamus da Burtaniya inda suka umarci shugaba Alexander Lukashenko da ya bayyyana inda Kolesnikova ta ke, bayan da wasu maza, wadanda ba a san ko su waye ba, sanye da takunkumi a fuskokinsu, su ka yi awon gaba da ita.