An Tsare Wasu Jami'an Gwamnatin Kasar Saudi Arabia

  • Ladan Ayawa

Prince of Saudi Arabia and Aleksandar Vucic

Kasar Saudiyya ta kame wasu jami'an gwamnatin ta hadi da wasu 'yan gidan sarauta kan zargin cin hanci da rashawa,wannandai ana yi ne da zummar samun daidait ga mulkin kasar.

Kasar Saudi Arabi ta kame wasu ‘yan gidan sarauta har su 11 ciki ko harda sanannen hamshakin mai kudin nan da kuma wasu da suke da mukamam minister ada da kuma yanzu.

Duka wannan nazuwa ne a kokarin da Matashin shugaban kasr Yarima keyi na samun daidaito a mulkin sa.

Haka kuma Sarki Salman ya matye gurbin shugaban sojojin tsaron kasa da akekira da turanci National Guard Yarima Miteb bin Abdullah wanda ada ake ganin shima yana cikin sahun masu neman sarautar kasar, shi da Babban Sojan ruwan kasar dama ministan tattalin arzikin kasa.

Kanfanin Dillacin Labarsai na Al-Arabia News wanda mallakar kasar ta SAudiyya ce ta fada cewa da yawan Yayan sarautar gidan kasar da aka tsare ciki ko harda Minista, anatsare dasu sakamakon tuhumar cin hanci da rashawa da ake binciken su akai kuma Yarima Mohammed Salman mai karfin ikon fada aji ne ke shugabantar kwamitin dake gudanar da wannan binciken.

Wannan kamen na mai kan uwada wabi yazo kasa da sati biyu bayan Yarima Mohammed ya gayyato dubban ‘yan kasuwa daga sasan duniya daban domin bajemusu manufarsa ta tattalin arzikin kasa da yake neman kaucewa dogaro da samun kudinshiga ta hanyan mai kawai.