Ana baiwa mata 6700, horo na sana’oin kala daban-daban wadanda aka jawo daga kananan hukumomi 44, a jihar Kano, bayan kammala horon gwamnati zata basu jarin kudin domin su fara sana’oin kansu.
Kwamishinan mata da walwalar jama’a ta jihar,Hajiya ‘Yar Dada Maikano Bich, ne ta furta haka a hirar su da Baraka Bashir, dangane da ire iren aiyukan da suke ke yi wa mata mussamam ma a bangaren dogaro da kai ta hanyar tallafi.
Ta kara da bayani dangane da matsalolin mata masu shaye shaye da aka rufe sansanin sun a dan lokaci domin gyara, inda tace a sansanin ana magance masu matsalolin shaye shaye da koya masu sana’oi, wanda daga bisani kuma a tallafa musu domin dogaro da kai.
Ta ce tallafi ne suke bayarwa ba bashi bane kyauta ne kuma akwai jam’ian da aka ware da suke sa musu ido wajen ganin basu cefanar da jarin da aka basu ba.
Jam’ian da suke bibiyar wandannan mata suna mika rahotonsu duk karshen wata domin duba nasarori da matsalolin da aka samu tare da lalubo hanyoyin da za’a magance matsaloli ko kuma akasin haka.
Ta kara da cewa babban matsalar da sukan fuskanta dai , shine ana son kyautata rayuwar mace an koya mata sana’a kwatsam sai wata matar dama tana da matsalolin gyara daki sai ta daukin wannnan kudi ta gyara gidanta na kyakyali maimakon sana’a.
Your browser doesn’t support HTML5