Jami'an tsaron Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo sun harba hayakin nan maisa kwalla a coci katolika dake birnin Kinshasa babban birnin kasar.
Sun yi haka ne da niyyar ganin sun hana su gudanar da wata zanga-zangar da aka shirya.
Masu zanga-zanga sun yi dafifi yau Lahadi a harabar cocin domin yunkurin gudanar da zanga-zangan nuna kin jinin shugaba Joseph Kabila.
Kasar ta Jamhuriyar Dimukaradiyyar Congo ta shiga rudunin siyasa ne tun lokacin da shugaba Kabila ya ki sauka akan karagar mulki.
Shugaban wanda a bisa tsari dokar kasar ya kammala wa'adin mulkinsa ne tun a cikin watan Disamban bara.
A lokacin ne ya kamata a ce kasar ta gudanar da wani sabon zaben shugaban kasa a cikin shekarar 2017, wanda hakan kuma ya kasa samuwa.
Wannan kememen da shugaban ya yi tare da jingine batun zabe ya kara harzuka ‘yan kasar ta Jamhuriyar Dimukaradiyyar Congo.