An Takaita Zirga Zirga a Jihar Borno

  • Ladan Ayawa

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima

An dauki irin wannan mataki dai shekaru ukku Kenan ana takaita zirga-zirgan abubuwan hawa a duk lokacin bukukuwan salla zuwa kirismeti

Gwamnatin jihar Borno tace ta takaita zirga-zirga akan bisa matakan tsaro ganin irin yadda akan kai hare-haren boma-bomai akan jamaa, wannansanarwan dai dake dauke da sa sakataren gwamnatin jihar Alhaji Jidda Shuwa.

Yace za a takaita zirga-zirgan ababen hawa ne har zuwa ranar lahadi, domin ganin an kare rayukan mutane da dukiyoyin jamaa.

An dauki irin wannan mataki dai shekaru ukku Kenan ana takaita zirga-zirgan abubuwan hawa a duk lokacin bukukuwan salla zuwa kirismeti, bisa matakan tsaro da hukumomin tsaron kasar ke dauka. Musammam ma da hukumomin tsaron ne ke bada wannan sanarwan.

Sai dai wannan sanarwan da ya fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar ya canza wannan salo na baya da yake fitowa daga wajen hukumomin sojojin kasar.

To ko Shin ko yaya al’ummar birnin Maiduguri keji da takaita zirga-zirga da hukumomin jihar keyi?

‘’Gaskiya ni zance bamu ji dadin abin ba dominidan ka lura kullun ana mutane a kulle a banza, da kyawon a bari sai anje sallar idi an dawo sai a bar mutane suyi ko kuma ayi yadda akeyi a Damaturu ba shiga ba fita, amma a cikin gari kowa ya wala’’

Amma shekara ukku ba za a canza abin ba idan ka duba wannan yaki da akeyi da taadancin nan har yanzu ba inda aka je don ba a canza salon yakin ba.

Ga Haruna Dauda da Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Borno - 2'21"