Rundunar ‘yan Samdan jihar Oyo, tare da rundunar tsaron farin kaya watau (Civil Defence) sun shirya tsaf domin samarda cikakken tsaro a lokutan bukukuwan sabuwar shekara 2017, mai kamawa.
Kakakin rudunar ‘yan Sandan jihar Oyo, SP Adekunle Ajesibutu, yace a cikin matakan da aka dauka harda girke jam’an ‘yan Sanda, a muhimman wurare da kuma hana buga (Knock Out) watau banga mai kara kamar bindiga a fadin jihar.
Ya ci gaba da cewa sun yin gargadi ga yara da iyayensu dasu nesanci buga banga, domin kaucewa razana jama’a, yana mai cewa duk wanda aka kama yana buga banga ko kuma wani laifi da dokar Najeriya, ta hana zai fuskanci gidan shara’a.
Shi kuwa kwamandan rudunar tsaron farin kaya a jihar ta Oyo, Mr. John Adewuye, ya baiwa jama’a, jihar tabbacin yin bukukuwan sabuwar shekara a cikin kwanciyar hankali.
Tuni dai rundunonin tsaron biyu, suka dauki matakai domin tabbatar da tsaron alokacin bukukuwan da bayan bukukuwan sabuwar shekarar.
Your browser doesn’t support HTML5