An Tabbatar Da Mutuwar Jami'an ‘Yan Sandan Mopol Shida A Wani Kwantan Bauna

Wasu yan bindiga

An tabbatar da mutuwar jami'an ‘yan sandan mopol shida, a wani kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yi musu a jihar Sokoto.

Ya zuwa yanzu dai an samu tabbacin mutuwar jami'an ‘yan sandan kwantar da tarzoma shida daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka yiwa kwanton bauna lokacin da suke rakiyar maniyata aikin Hajji a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban karamar hukumar Isa Abubakar Yusuf Dan Ali da dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Habibu Halilu Modaciya, sun tabbatar da mutuwar mutanen shida.

Ganin yadda matsalolin rashin tsaro suka tabarbare a yankin, dan majalisar ya shawarci jama'a da su kauracewa hanyar Isa zuwa Gundumi.

Wannan hanyar dai akan ta makon da ya gabata aka fara tare uban kasar Bafarawa inda aka yi garkuwa da yaransa biyu.

A hirar shi da Muryar Amurka, babban kane ga uban kasar Nasir Dalhatu Bafarawa ya tabbatar da sako yaran amma bai yi karin bayani game da yadda aka sako su ba.

Matsalolin rashin tsaro dai na ci gaba da tayar da hankulan ‘yan Najeriya duk da kokarin da mahukunta ke cewa suna yi na shawo kan matsalolin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An Tabbatar Da Mutuwar Jami'an ‘Yan Sandan Mopol Shida A Wani Kwanton Bauna Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Musu