A wani a taron manema labarai, Babban Sakataren gwamnatin Najeriya kana kuma shugaban kwamitin ko ta kwana na shugaban kasa da ke yaki da cutar coronavirus a kasar, Boss Mustapha ya tabbatar da cewa mutane 684 ne suka kamu da cutar COVID-19 daga cikin mutane 13,844 wadanda aka gwada kuma kaso 80 cikin 100 a cikinsu matasa ne.
Izuwa yanzu dai mutane 14,906 ne aka yi nasarar dawowa da su kasar daga kasashen ketare.
Da aka tambaye shi kan sanin wasu hanyoyi ko dabaru dake bi wajen tantance wadannan mutane ne, Shugaba dake lura da tsare-tsare na kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar a kasar baki daya, Dr Sani Aliyu, ya bayyana a rubuce cewar bashi da masaniya kan cikakken adadin mutanen amma kaso 5 cikin 100 na wadanda aka dawo da su kasar a jirage mabanbanta cikin wannan lokaci na annobar, sakamokon gwaji ya tabbatar suna dauke da cutar duk kuwa da gwajin da aka yi musu kafin a dawo da su kasar ya yi nunin akasin haka, kuma sai sun sake bin matakai na killace kai na tsawon mako biyu da kuma basu kulawa yanda ya kamata.
Shi ma mai magana da yawun kungiyar 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM Rasheed Balogun ya shaida haka.
Kazalika, Dan Majalisar Dokoki Na Tarayya, Dr Yusuf Tanko Sununu na jihar Kebbi kana shugaban kwamitin lafiya na Majalisar Wakilai na kasar ya yi kari da cewar hakan.
Daga karshe gwamnatin Najeriya ta yaba wa shugaban Amurka Donald Trump bisa alkawarin da ya yi na taimaka wa kasar da kayakin aiki na yaki da cutar, kama daga na’urar taimaka wa numfashi wato 'Ventilators' guda 200 da dai sauransu.
Saurara karin bayani daga Shamsiyya Hamza a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5