An Tabbatar Da Bullar Cutar Sankarau a Jihar Katsina

Cutar Sankarau

Ma’akatar lafiya ta jihar Kastina ta tabbatar da cewa mutane fiye da 300 ne suka kamu da cutar sankarau, kuma 30 sun mutu sanadiyyar cutar.

‘Yan makonni da suka gabata cutar sankarau ta hallaka mutane 13 a wani kauye mai suna Majiya dake yankin karamar hukumar Taura dake jihar Jigawa.

Babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta Katsina, Dakta Kabir Mustafa, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, tun a watan Janairun bana cutar ta bulla wasu sassan jihar, kuma a makonni biyu da suka gabata ta hallaka mutane 8 a yankin karamar hukumar Jibiya.

Dakta Kabir, ya koka kan yadda jama’ar yankunan karkarar jihar ba sa kai rahotan samun cutar sankarau ga cibiyoyin lafiya mafi kusa, amma ya ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da kungiyoyin agajin kiwon lafiya na ketare na aiki tare domin magance matsalar.

A jihar Jigawa kuwa cutar ta sankarau ta kashe a kalla mutane 13 a garin Majiya na karamar hukumar Taura, baya ga mutane fiye da 50 da suka kamu da cutar.

Yanzu dai ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina ta ce ta fara aikin bada magungunan rigakafin cutar ta sankau ga mutane da ba su kamu da cutar ba, amma rahotanni sun tabbatar da cewa, hukumomi a jihar Jigawa ba su kai ga daukar makamancin wannan mataki ba tukunna.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tabbatar Da Bullar Cutar Sankarau a Jihar Katsina - 3'32"