Sakamakon zaben ya ba shugaban kasar Dennis Sassou Nguesso damar sake neman takarar shugabancin kasar karo na uku.
Sakamakon da ya fito a hukumance ya nuna kaso 92 na masu zaben kwaskwarimar ya haifar da sakamakon da kashi 72. ‘Yan adawa dai tuni suka juyawa zaben baya da cewa mutane kadan ne suka fito zaben.
Shugaban ‘yan adawar kasar Pascal Tsaty Mabiala yayi kira da ayi watsi da wannan zaben kada kuri’ar kwaskwarimar.
A wani rahoton da ya shafi zabe a kasar Ivory Coast kuma, a jiya Talata ake sa ran hukumar zaben kasar zata bayyana sakamakon farko na zaben da aka yi.
Zaben da ake kyautata zaton zai bawa Shugaban kasar Alassane Ouattara wani wa’adin shugabanci. Hukumar ta kiyarsa kimanin kasha 60 cikin 100 na masu kada kuri’a ne suka fito zaben .
Sai dai kungiyoyin fafaren hula sun bayyana cewa da kaso 53 za a danganta fitowar jama’a. jam’iyyar adawa ta National Coalition for Change ta tababar fitowar.
Sun bayyana cewa, mafiya yawan ‘yan kasar sun yi zamansu ne a gida ba tare da fita zaben ba, wanda hakan ya nuna wadanda suka yi zaben ba su wuce kaso 20 kacal ba.
4C: Suma a kasar Tanzania, dan takarar jam’iyya mai mulkin kasar John Magufuli yana kan gaba a jiya Talata, amma mafi yawancin ‘yan majalisar Ministocin kasar sun rasa kujerunsu.
Bisa ga yadda kidayar zaben kasar da aka gudanar a ranar Lahadi take tafiya. Ministocin sun rasa samun nasarar dan takarar su a bangaren gamayyar ‘yan adawa ciki har da CHADEMA.
Wadda itace babbar ‘yar adawar jam’iyyar CAMA CHA MAPINDUZI ko CCM a takaice da ta dade tana mulki. Ana sa ran zaben shine mafi tsanani a tarihin zabukan kasar, inda CMM ke fuskantar kalubale a karon farko cikin shekarun da tayi tana mulki.