An Soma Horas Da Maniyata a Jihar Gombe

Alhazan da suka taru kusa da birnin Makka mai tsari a Saudiya

A jihar Gombe maniyata zuwa Saudi Arabiya suna samun horo akan rukunin ayyukan hajji da zasu basu damar gudanar da aikin ibadar yadda ya kamata.

Hukumar alhazai ta jihar Gombe ke gudanar da shirin ilimantar da maniyatan akan mahimman ayyukan da zasu gudanar a lokacin da suka isa kasa mai tsarki domin rage rudani.

Uztas Mukhtar Musa Danboyi jagoran malaman dake horas da maniyatan yayi karin bayani. Yace ana koyas da ayyuka na hajji da Umurah da kuma ziyara ta Manzon Allah (S.A.W.). Ana karantar da mutane akan tarbiya irin ta addinin musulunci da tarbiyar zamantakewa a cikin kasa mai tsarki, wato a garin Makka da na Madina.

Wasu ana cutarsu wajen canji amma suna cigaba da wayarwa alhazai kai da yanayin kiwon lafiya da duk abun da zai taba tarbiyan alhaji, ko kasar Saudiya ko kuma kasar Najeriya.

Su ma maniyatan sun bayyana gamsuwa game da irin koyaswa da suke samu. Anfanin horon yana da yawa. Malaman dake koyas dasu sun yi masu yadda zasu fahimta. Karantarwar ta shafi ibadun maniyatan ne gaba daya ba wai sai abun da ya ta'allaka da aikin hajji ba.

Malam Usman Gurama babban sakataren hukumar alhazai ta jiha ya bayyana irin tanade-tanade da aka shiryawa alhazan a can kasar Saudiya. Yace sun sami gidaje kusa da harami kuma na zamani. Kana kuma sun yi shirye-shirye akan maganar abinci a Minna wanda ana korafe-korafe a kansa. Amma bana, inji shi, sun zauna da kamfanin da zasu yi masu abinci. Sun yi yarjejeniya kuma sun amince. Alhazan kimanin dubu biyu zasu ji dadin ayyukan hajjin bana.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

Your browser doesn’t support HTML5

An Soma Horas Da Maniyata a Jihar Gombe - 3' 03"