A ranar Asabar mai zuwa ne al’umar jihar Kano zasu kada kuri’a domin zaben Shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a kananan hukumomin jihar ta Kano 44. A jiya hukumar zaben jihar ta shirya bita ta musamman ga kungiyoyin da zasu sanya idanu akan yadda zaben zai wakana.
Taron bitar na daga tsare tsaren da hukumar zaben ta jihar Kano ke yi domin tunkarar zaben na ranar Asabar. Tuni dai hukumar ta hada hannu da zauren gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Kano domin tabbatar da nasara. Comrade Ibrahim Wayya dake zaman shugaban zauren ya fayyace muhimmancin taron bitar na yau.
Kwamrad Kabiru Sa’idu Dakata na cikin wadanda suka gabatar da makala a wurin taron wanda ya wakana a cibiyar bincike kan harkokin demokaradiyya ta Mambayya a nan Kano. Kodayake Shugaban Hukumar zaben jihar ta Kano ya bayyana cewa, jam’iyyu 12 ne za su fafata a zaben na ranar Asabar, amma an fi jin amon Jam’iyyun PDP da APC a yankunan kananan hukumomin jihar 44, inda za a zabi shugabannin kananan hukumomin guda 44 da mataimakansu da kuma kansiloli 484.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5