Kungiyar Waiwaye mai cibiya a Kano wadda ke rajin raya al’adu da tsarin rayuwar Hausawa ta shirya lacca da ta saba gudanarwa shekara-shekar domin tattauna al’amuran da suka shafi zamantakewar al’umar Hausa a lokutan baya da kuma makomar al’adun Bahausashe a wannan zamani.
Taken laccar na bana shine rayuwar Bahausashe kafin zuwan Turawa da Larabawa kasar kasar Hausa.
Malam Ibrahim Muhamamd Mandawari dake zaman shugaban kungiyar ta Waiwaye a nan Kano ya fayyace dalilai da kuma manufar shirya taron laccar da kuma zabar taken ta na bana.
A cewarsa ya kamata Bahaushe ya san daga ina yake. Yanzu a wane matsayi yake sannan ina zashi. Mutumin da bai san inda ya fito ba ba zaisan inda zashi ba. Tun kafin hasken Musulunci ya isa kasar Hausa, harshen ya fara wanzuwa. Ya yi gargadin kada a bari a sake komawa cikin duhun jahilci.
Manyan malamai da masana tarihin rayuwa da al’adun kasar Hausa da Hausawa ne suka suka yi tsokaci a yayin laccar.
Dr Muhammad Tahir wato Baba Impossible na Jami’ar Bayero Kano wanda ya gabatar da Makala a wurin taron, ya ce kodayake harshen Hausa ya samu daukaka ta hanyar yaduwa a sassan duniya, amma sana’o’i da al’adun Bahaushe sun samu koma baya sakamakon cakuduwar su da sauran kabilu.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun bayyana gamsuwa da irin abubuwan da suka ji a wurin taron.
Sarakunanan gargajiya da manazarta kan harshen Hausa da al’adun Hausawa a Jami’o’i da cibiyoyin harkokin ilimi ne suka halarci taron.
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5