Hukumar zaben Najeriya ta INEC, ta ce an shigar da kararraki 807 a kotunan karar zabe, biyo bayan zaben 2019 da a ka gudanar.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a taron karshe na kwamishinonin hukumar na jihohi.
A cewar shi, cikin adadin kararraki 807 an kori 582, masu kara kuma sun janye 183.
Farfesa Yakubu ya ce bisa hukuncin kotu, hukumar zaben za ta sake zabe a mazabun wasu ‘yan majalisar dattawa, da wakilai da suka kai 30.
Jami’in yada labaran hukumar, Aliyu Bello, ya ce kararrakin ba sabon abu ba ne, in an duba zabukan baya.
A ra'ayin masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Farouk B.B Farouk, da wuya a samu hujjar kalubalantar zabe a kotu.
Saurari rahoto cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5