An shiga Yini Na Uku Da Katsewar Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Najeriya

Tashar wutar lantarrki a Najeriya (Facebook/ Ministry of Power Nigeria)

Kamfanoni 12 ne kawai ke aikin sarrafa wutar lantarki a kasar, bayan samun raguwar Ƙarfin wutar daga megawatts dubu 3 zuwa dubu 1,758.

ABUJA, NIGERIA- Akalla kwanaki uku kenan da wasu birane a Najeriya suka auka cikin duhu sakamokon lalacewar tushen wutar lantarkin kasar

Bayanan da a ke samu na nuni da cewa an samu matsala ne a manyan cibiyoyin samar da wutar inda adadin wutar da za a iya rabawa a kasar ta zama ta sauko kasa ainun.

Kamfanoni 12 ne kawai ke aikin sarrafa wutar lantarki a kasar, bayan samun raguwar Ƙarfin wutar daga megawatts dubu 3 zuwa dubu 1,758.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani jami’in a daya daga cikin masana’antu samar da wutar lantarki a kasar na cewa an samu rugujewar na’urorin wutar lantarki da dama a jiya Talata, daga tasoshin wutar lantarkin da ke amfani da iskar gas a lokacin da ake kokarin samar da wutar lantarki zuwa babban birnin tarayyar kasar Abuja ta hanyoyin tashoshin wutar lantarki guda uku da ake da su, wadanda suka hada da magudanan ruwa na Kainji, Jebba da Shiroro duk a jihar Naija dake yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

Binciken masana'antu 12 da ke aikin samar da wutar lantarkin ya yi nuni da cewa na’urorin sun yi ta aiki har zuwa karfe biyar na yammacin jiya akan megawatts dubu 1,758 kafin daga bisani suka dauke baki daya, lamarin da ya haifar da daukewar wutar.

A yanzu haka dai ana samun matsaloli biyu a lokaci guda a babban birnin Najeriya Abuja, inda har yanzu ake fuskastar wahalar mai da ya haifar da dogayen layin neman fetur ga karancin wutan lantarki wanda ya jawo abubuwa suka yi tsaya cak har a harkokin gwamnati inda ma’aikatu ke tashi da wuri sakamokon rashin wutar lantarkin.

Kazalika, wannna matsala ta shafi 'yan kasuwa da dama, musamman suke dogaro da wutar lantarki wajen gudanar da harkokinsu.

Ko da yake dai tun a daren ranar Litinin Ministan wutar lantarki a kasar Injiniya Abubakar .D. Aliyu ya kira wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki don shawo kan matsalar.