Biranen Sydney na kasar Austireliya da Auckland na kasar New Zealand sun kaddamar da nasu bukukuwan da baje kolin tartsatsin wuta
A Najeriya, shekarar 2025 na daf da shigowa kuma kamar yadda yake bisa al’ada, dimbin ‘yan Najeriya, musamman Kiristoci zasu shafe sa’o’in karshe na 2024 a majami’u, inda zasu gudanar da addu’o’i da wake-wake da raye-raye tare da ihun “muna murnar sabuwar shekara” a daidai lokacin da babban hannun agogo ke hawa kan minti guda kafin shiga 2025.
Mai yiyuwa wadanda ba Kiristoci ba su tafi sauran wuraren holewa da ke fadin kasar domin yin shagulgulan shiga sabuwar shekarar.
Wuraren farko da suka fara kada kararrawar shiga sabuwar shekarar sune tsibiran kiribati dana kirsimeti, wadanda tuni suka shiga shekarar 2025.
Habasha da Nepal da Iran da kuma Afghanistan ne kasashe 4 da ba za’a gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekarar 2025 a cikinsu ba.