Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa, karkashin jagorancin Janar Theophilus Yakubu Danjuma mai ritaya, da aka azawa nauyin sake tsugunarda 'yan yankin wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita, ya fara samun shawarwari kan yadda zai taimakawa mutanen yankin.
Da yake magana kan yadda ayyukan kwamitin zai taimaka, musamman wajen sake ginawa mutane gidajensu, tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatin marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua, Alhaji Abdulrahman Adamu, yace kwamitin yayi la'akari da yanayi da kuma al'adun mutanen.
Tsohon ministan yace, ba zai dace ba ace an ginawa mazauna kauyuka irin gidajen da suke alkariya.
Shima da yake magana, dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Adamu kamale, ya roki kwamitin yayi aiki tsakaninsa da Allah ba tareda nuna son zuciya ko zarmiya ba.
Kamale, ya bukaci kwamitin ya maida hankali sosai kan bukatun hanyoyi, wadanda yace barnar da 'yan binidgar Boko Haram suka yi ya karya gadoji da lalata hanyoyin sufuri.
Dan majalisar yace yanzu haka ba za'a iya jigilar abinci zuwa yankin Michika da Madagali ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5