An Sauya Sunan Wani Yanki a Senegal Saboda Mutuwar George Floyd

Shugaban kasar Senegal Macky Sall

Mutuwar George Floyd a hannun 'yan sanda wato ba'amurken nan bakar fata da fafutukar neman a rika ba rayukan bakaken fata muhimmanci, sun sa wani yankin kasar Senegal ya sauya sunansa.

Wani karamin tsibiri da ke gefen gabar tekun Afirka wanda aka san shi da rawar da ya taka a lokacin cinikin bayi, ya canza sunansa sakamakon mutuwar George Floyd da kuma fafutukar jaddada muhimmacin rayukan bakaken fata ta “Black Lives Matter “ da ake yi a duniya.

Tsibirin Goree, mai nisan ‘yan kilomitoci daga gabar tekun Senegal, ya ba da sanarwar a jiya Talata cewa, yankin da aka sani da "Yankin Turai" ko kuma “Europe Square” a turance za a canza sunansa zuwa “ Freedom and Human Dignity Square” a turance, wato dandalin ''Yanci da Mutunta dan Adam” bisa shawarar da majalisar gudanawar yankin ta yanke.

Sunan yankin ya samo asali ne a shekarar 1998 bayan da wasu kudade da nahiyar turai ta bayar wajen sake gina shi wanda yana daya daga cikin wuraren da hukumar adana kayayyakin tarihi ta UNESCO ta ware a matsayin wajen tarihi.