Ga bisa dukkan alamu rigima na neman ta kunno kai a cikin kungiyar kwadago ta Nigeria, yayin da daya bangaren ke kiran ma'aikata su shiga yajin aiki, daya bangaren ko cewa yake yi ma'aikata suyi biris da wannan kiran.
WASHINGTON DC —
Kungiyar ULC tace ta umurci ‘ya’yanta da su fara yajin aikin daga yau Litinin.
Kakakin kungiyar ta ULC Nasir Kabir yace zasu ci gaba da yajin aikin na “har sai abinda hali yayi” har sai shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministanKwadago wanda ya zarga da fakewa da bazar shugaban kasar yana yiwa ma’aikata rashin adalci.
Sai dai a waje daya kuma, shugaban kungiyar kwadago ta NLC Ayuba Waba yace kungiyar ta ULC ba sananniya bace kuma bata da rajista.
Yace kungiyar NLC ta umurci ma’aikata suyi biris da wannan kiran na ULC.
Ga Hassan Maina kaina da Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5