An Samu Rangwame Akan Farashin Kujerar Zuwa Aikin Hajjin Bana

Shaikh Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar IZALA

Bana an samu rangwame farashin zuwa aikin hajji bisa ga ta bara, amma har yanzu ana nemangwamnatin tarayya ta saukar da farashin canjin dala

Masu ruwa da tsaki akan aikin hajji a Najeriya na ci gaba da yin tsokaci bayan da hukumar alhazan kasar ta ayyana kudin kujerar zuwa hajji bana, wato shekarar 2018.

Kamar yadda aka yi bara kowace jiha na da tata farashin kujerar amma a wannan shekarar an samu saukin farashin kujerar akan na bara.

Bana Naira miliyan daya da dubu dari hudu da sittin da biyar da dari biyar (N1,465,500) kowane Alhajin jihar Neja zai biya. Akan farashin na bara an samu saukin Naira dubu hamsin da daya da dari biyar (N51,500).

Shugaban kungiyar IZALA a Najeriya Shaikh Abdullahi Bala Lau ya ce saukin bai isa ba. Ya yi kira ga hukumar alhazai ta kara dubawa domin a kara sassauci.

A na shi gefen shugaban kungiyar dalibai musulmi a Najeriya Jamilu Muhammad Jamil ya ce duk da haka sun ji dadi. Akwai dan kwantar da hankali domin abun da alhazan bana zasu biya bai kai na bara ba. Ya yi fatan za’a ci gaba da samun ragowa. Sai dai ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara rage farashin dalar.

Sakataren hukumar alhazan jihar Neja Shehu Barwa Beji ya bayyana dalilin da ya sa aka samu dan saukin. Yace gwamnan jihar ya amince ya dauke biyan kudaden jakuna, gwamnati ce zata biya wannan.

Ita ma hukumar jin dadin alhazan jihar ta ce ta dauki matakin dakile duk wata cuwa-cuwar damfarar maniyatta kamar yadda wani jami’in hukumar Umar Maku Lapai ya bayyana. Babu wani ma’aikacin hukumar da aka ba izinin ya karbi kudi daga wani Alhaji. Ma’aikatan karamar hukuma ke da wannan hakkin. Duk wani ma’aikacin hukumar alhazai da ya karbi kudi za’a hukunta shi.

Jihar ta samu daya daga cikin naurorin da hukumar alhazan Najeriya ta raba domin gudanar da tantance lafiyar alhazan kamar yadda hukumomin Saudiyya suka nemi a yi.

A saurari karin bayani a rahoton Mustapha Masiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Ragwame Akan Farashin Kujerar Zuwa Aikin Hajji Bana – 2’ 58”