Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da shan miyagun kwayoyi mai helkwata a Vienna da hadin gwiwar ofishin kididdiga na Najeriya, sun baiyana cewa an samu raguwar yawaitar neman cin hanci da rashawa a Najeriya, amma ba a samu raguwar karbar cin hancin ba.
Nazarin mai shafi 112 ya nuna cewa an samu raguwar cin hancin daga shekarar 2016 daga kashi 32.3% zuwa kashi 30.2%.
Rahoton ya zanta da iyali dubu 33 a dukkan jihohin Najeriya, inda ya gano fiye da kashi 30 cikin 100 na mutane an tambaye su sun ba da cin hanci ga jami'an gwamnati don samun aiki ko wata alfarma.
Sashin arewa ta tsakiya da kudu maso kudu da kudu maso gabas sun samu karuwar cin hanci da rashawa.
Binciken ya duba yadda tasirin cin hancin ke barazana ga nasarar alwashin gwamnatin Najeriya na fitar da mutum miliyan 100 daga talauci zuwa shekarar 2030.
A zahiri dai tamkar a na tubka da warwara ne, kan yakin ko kuma hannun dama ya kwato na hagu ya kwace.
Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hancin Ibrahim Magu ya nanata cewa hukumar sa na samun nasara kan yakin.
In za a tuna Barista Aminu Gamawa a wajen taron bitar yaki da cin hanci na hukumar ta EFCC, ya ce sai an hukunta 'yan bora da 'yan mowa har dai yakin zai samu nasara.
Shugaban hukumar kididdiga ta Najeriya Yemi Kale da wakilin cibiyar yaki da miyagun kwayoyi ta MDD, Dr. Oliver stolpe su ka sanya hannu kan rahoton da ya ce fiye da rabin 'yan Najeriya sun yi amanna da cewa shekaru biyu gabanin binciken cin hancin ya karu ne.
Da alamu dai rahoton ya yi sara da duba bakin gatari.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya cikin sauti.