An Samu Na’urar Dake Maganin Ciwon Damuwa

Larurar damuwa babbar matsala ce da ke shafar kwakwalwa, ciwo ne da ke rikitar da rayuwar dan Adam.

Wasu lokutan wannan yanayin larurar yakan sa mutum ya ji ba shi da wata daraja, har ya kan yi tunanin kashe kansu.

Wasu mutane suna samun saukin ciwon damuwa idan suna shan magani, wasu kuma suna samun sauki idan sun je wurin kwararrun ilimin kwakwalwa da ilimin dan Adam don taimaka musu da shawarwari. Amma irin wadannan jinya ba ko da yaushe ta ke aiki ba.

Abin farin ciki shine akwai wani yanayi na jinya da mutane zasu iya gwadawa.

Jami’ar Missouri, bangaren kula da lafiya, ya samo wata na’ura da zata magance wannan larurar ta damuwa, abinda ake kira Transcranial Magnetic Stimulation da turanci, ko kuma TMS a takaice, wannan na’urar ba sai anyi fida ba, ko allurar sa baci da ake kira “Anesthesia”.