Ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda ta tabbatar da cewa wani yaro dan shekaru biyar da haihuwa ya kamu da cutar Ebola, lamarin dake nuna a karon farko cutar ta yadu zuwa wata ‘kasa, yaduwar da ake gani a matsayin mafi girma ta biyu a tarihi.
Yaron dan asalin kasar Congo, ya isa kasar Uganda ranar Lahadi shi da iyalansa, kuma an kebe shi a Asibitin Kesese, birnin dake kan iyaka da jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.
Wannan labari na zama tamkar koma baya ne ga ma’aikatan lafiya da suka kwashe watanni suna yaki da yaduwar cutar zuwa wasu kasashe daga Congo, inda sama da mutane 2,000 suka kamu da cutar a cikin watanni goma da suka gabata. Kusan mutane 1,400 cikinsu sun mutu.
Ma’aikatan agaji daga hukumar kare yaduwar cututtuka ta Amurka CDC da hukumar raya kasaseh masu tasowa USAID, sun yi ta horarwa da tare da bada rigakafi ga ma’aikatan lafiya a kasashen irin su Uganda da Rwanda da kuma Sudan ta Kudu, baki ‘daya kasashen makwabta ne ga kasar Congo wadda ke fama da cutar.
Tun shekarar 2013 ne annobar cutar Ebola ta barke, ta kuma kwashe kusan shekaru uku, ta yi sanadiyar rayukan mutane sama da 11,000 a kasashen yammacin Afirka.