A dai dai lokacin da yan kasa ke fatan ganin majalisar dokokin Najeriya ta kammala aiki akan kasafin kudin bana, sai wata sabuwa ta kunno kai, inda shugabannin kwamitocin majalisar Wakilai da na Dattawa, dake kula da kasafin kudin sukace an gono kura-kurai da yawa da zai kawo koma baya ga aikin da ake yi aka kasafin kudin.
Shugaban kwamitin majalisar Dattawa dake kula da kasafin kudi Dan Juma Goje, yace “akwai rudani da yawa a cikin kasafin kudin, sai muka ga ba yadda zamuyi muyi aikin mu kamar yadda tsarin mulki ya bamu na cewa idan shugaban kasa ya kawo mana tsarin kasafin kudi, mu dube shi bisa tsarin doka.”
Ya ci gaba da cewa akwai rudani da yawa ciki don yanzu haka ma sai an sake rubuta tsarin daga farko, ya kuma suna mai sanar da jama’a cewa kada aga lokacin da ake tsammani na sati biyu ya cika ba tare da an fitar da komai ba, a kuma fara zargin ‘yan majalisa.
Bincike da wakiliyar Muryar Amurka Madina Dauda, ta gudanar ya nuna cewa an sami karin Naira Biliyan Goma a kasafin kudin ma’aikatar ilimi, wani abu da yan majalisar suka ce bazai sabu ba bindiga a ruwa, sauran ma’aikatu da aka sami kura kurai a kasafin su sun hada da ta ma’aikatar Kiwon Lafiya da ta Sufuri da ta Ayyuka da kuma ta Kimiyya Da Fasaha.
Don karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5